Hawa Tsauni Mafi Tsawo dake jihar Taraba Najeriya

Sauti 10:20

A wani yunkuri na hawa tsaunin da ya fi kowanne tsawo a yankin Afurka ta Yamma, an tara gwanaye sama da dari daga kasashe daban-daban domin hawa tsaunin Chappal Wadei dake cikin jihar Taraba a Tarayyar Najeriya. Za a dauki kwanki goma sha uku ana wannan kokarin hawa tsaunin. Alhaji Usman Abubakar Mahmud Gumi, shine jagoran shirya wannan kokari, tare da taimakon injiniya Charles.A shekaru biyu da suka shude, Alhaji Usman Gumin ne ya ka kawo wasu Turawa daga kasar Latviya, suka kuma hau Dutsen Zuma, wanda ake cewa ya gagari duk wanda ke da azamar hawansa a baya.