Nigeria

Mutane 163 sun rasa rayukansu sakamakon shakar guba

Mutane 163 suka mutu a Nigeria, sakamakon shakar guba, a inda ake hakar ma’adinin gwal, dake Jihar Zamfara.Wani jami’in lafiya, a ma’aikatar lafiyar kasar, Henry Akpan, yace sun tabbatar da mutuwar mutane 163, cikinsu harda yara 111, a cikin watanni biyar da suka gabata.Jihar Zamfara na da arzikin ma’adinin gwal, wanda jama’a ke hakarsa ba tare da izini ba.