Nigeria

Wole Soyinka Zai Kafa Jamiyyar Siyasa

Farfesa Wole Soyinka
Farfesa Wole Soyinka RFI Hausa

Shahararren marubucin nan dake Najeriya Farfesa Wole Soyinka wanda ya taba samun kyautan Nobel na gwanancewa wajen rubuce-rubuce ya bayyana shirin sa na kafa jamiyyar Siyasa.A tattaunawa da sashen Hausa na Radiyo Faransa- RFI, Farfesa Wole Soyinka bai ce ga ainihin sunan jamiyyar siyasar ba tukuna.Shi dai Farfesa Wole Soyinka na bukukuwan cikan sa shekaru 76 ne yana raye a duniya.A cewar sa ba wannan ne karonsa na farko ba daya shiga jamiyyar Siyasa domin cikin janhuriya ta biyu ya kasance dan jamiyyar PRP ne tare da Balarabe Musa.Yace a wancan lokaci har ya riki wani mukami karami cikin jamiyyar.Yace a koda yaushe ya kan bada goyon bayan sa ga jamiyyar da take da manufofi masu kyau.Ta haka ne yace zaa yaki raayoyi marasa amfani ga jamaa.