Muhallinka Rayuwarka

Gubar Dalma Na Cigaba da Kisa A Zamfara

Wallafawa ranar:

Daruruwan kananan yara na cigaba da mutuwa sakamakon cutar gubar dalma a jihar Zamfara, duka da cewar an share fiyeda watanni 6 ana fama da wannan matsalar, bayan makuddan kudaden da hukumomi a jihar Zamfaran suka bayyana sun kashe akan wannan mtsalar. Dangane da wannan ne wakilinmu a Sakkwato Faruk Muhammad Yabo, ya hada mana wannan rahoton.