Najeriya

Rikicin kan rohoton Wikileaks

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan

Yanzu haka takaddama ta kaure tsakanin fadar shugaban Nigeria, da kakakin Majalisar wakilai, Dimeji Bankole a bangare guda, da kuma Jaridar NEXT a bangare guda, kan wani rahotan Wikileaks da aka ruwaito shugaba Goodluck Jonathan, ya kada kuri’a sau hudu yayin zaben shekara ta 2007, da kuma zargin cewa, kakakin Majalisar wakilai Dimeji Bankole, ya ce an baiwa alkalan kotun koli cin hanci dan hanasu soke zaben Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua.Tuni bangarorin biyu sun yi watsi da rahotan.