Najeriya

An hallaka wani Malamin Islama a Garin Maiduguri

Wasu 'yan bindiga a garin Maiduguri, fadar gwamnatin Jihar Borno, sun kashe wani limami a gidan sa, a cigaba da kisan mummuken da ake birnin.Rahotanni sun ce an kashe Malam Ibrahim Abdullahi Gomari , wanda ake ganin na kusa da mataimakin gwamnan jihar ne, ne a gidansa, kuma ana zargin kungiyar Boko Haram da aiwatar da kisan, wadda ke da alhakin mutane mutane masu yawa tun shekara ta 2009.