Najeriya

Rikici na karuwa yayin da ake shirin zaben Najeriya

CIA

Tashin hankalin da ake samu wajen yakin neman zabubukan Najeriya masu zuwa, yanzu haka ya lakume rayukan mutane sama da 90, yayin da wasu sama da 200 suka samu raunuka.A Jihar Gombe, an zargi magoya bayan Jam’iyar CPC da lalata ofishin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan, amma wani jigo a ofishin yakin neman zaben shugaban kasar, kuma Dan Gwambe, Habu Mu’azu, ya wanke CPC daga lalata ofishin. Inda ya zatgi magoya bayan gwamna Danjuma Goje, kamar yadda ya shaida wa gidan rediyon Faransa.