Nigeria

An rantsar da sabuwar Ministan kudi a Nigeria

Ministan kudin Nigeria Ngozi Okonjo-Iweala
Ministan kudin Nigeria Ngozi Okonjo-Iweala

A Nigeria, an rantsar da Mrs Ngozi Okonjo-Iweala, a matsayin ministan kudin kasar.Rantsar da sabuwar ministan zai sanya wa ‘yan kasar fatan ganin an sami yalwar tattalin arziki a kasar, ganin cewa Mrs Okonjo-Iweala, kwararriya masaniyar tattalin arzikin kasa ce. Tana daya daga cikin wadanda shugaban kasar Goodluck Jonathan ya zaba a matsayin Ministocin shi, tun bayan da ya lashe zaben da aka yi a kasar a farkon wannan shekarar.Ta dai ajiye aikin ta a matsayin Darakta a Bankin Duniya don ta bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar tata, da cin hanci da rashawa suka dabaibaye.A baya, Mrs Okonjo-Iweala ta rike mukamin ministan kudin kasar karkashin gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, daga shekarar 2003 zuwa 2006, inda aka yaba mata, saboda yadda ta yi ta kai gwauro tana kai mari, har sai da aka yafe wa kasar dumbin basukan da a da, suka mata katutu.Ta kuma rike mukamin ministan harkokin wajen kasar na wani dan takaitaccen lokaci.Babban kalu balen da ke gaban sabuwar ministan shine taimakawa wajen fidda miliyoyin ‘yan kasar daga kangin talaucin da ya musu katutu, a kasar da ke samun fiye da kashi biyu cikin 3 na kudaden shigar ta daga cinikin man fetur da take tonowa.