Nigeria

Sojoji ba za su bar Plateau ba

Sojoji a Jihar Pilato, Nigeria
Sojoji a Jihar Pilato, Nigeria

RUNDUNAR Dake aikin samar da Tsaro, tace har yanzu tana nan a Plateau, kuma shugaban kasa ne kawai zai iya janye su.Kakakin rundunar, Manjo Charles Ekeocha, yayi Karin haske akai.har yanzu muna nan, Gwamnatin Tarayya ce ta kawo mu, saboda haka ficewar mu anan, zai fit one daga Gwamnatin Tarayya, ina so in shaida maka, wannan rundunar na nan ne, saboda Gwamnati na bukatar mu anan, idan suna da matsalolin su, su je su sasanta a tsakanin su, amma kar su jefa mu cikin siyasa, abin bakin ciki ne mai hankali zai nemi jefa soja cikin siyasar Jiha.