Bankin Duniya

Za’a zabi shugaban Bankin Duniya tsakanin Ngozi da Dan takarar Amurka

Jim Yon Kim, da  Ngozi Okonjo-Iweala, wadanda zasu fafata a zaben shugabancin Babban Bankin Duniya
Jim Yon Kim, da Ngozi Okonjo-Iweala, wadanda zasu fafata a zaben shugabancin Babban Bankin Duniya REUTERS/Issei Kato/Nicky Loh - Montage RFI

Shugabannin Bankin Duniya zasu gudanar da taro domin zaben wanda zai jagoranci Bankin, tsakanin Dan takarar Amurka Jim Yong Kim da Ngozi Okojo Iweala ta Najeriya bayan Antonio Ocampo na Colombia ya janye takarar shi.

Talla

Wannan ne karo na farko da Dan takarar Amurka zai fuskanci kalubale daga kasashe masu tasowa bayan kwashe shekaru 66 Amurka na shugabancin Babban Bankin.

Sai dai har yanzu ana Tunanin dan takarar Amurka zai samu goyon bayan kasashen Turai da Japan masu yawan hannun jari a Babban Bankin.

A ranar Juma’a ne tsohon Ministan kudin kasar Colombia Jose Antonio Ocampo ya jingine takarar shi, bayan zargin tasirin siyasa a zaben shugabancin Bankin. Yanzu Ngozi Ministan Kudin Najeriya ita ce zata fafata da Kim Yong Kim.

Akwai dai hasashen Brazil da Rasha da India da China zasu mara wa Ngozi baya wacce tsohuwar Ma’aikaciya ce a babban Bankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.