WHO

Daruruwan mutane ke mutuwa sanadiyar zazzabin cizon sauro a Najeriya

Wata mata dauke da yaronta mai fama da cutar Zazzabin cizon sauro
Wata mata dauke da yaronta mai fama da cutar Zazzabin cizon sauro Spencer Platt/Getty Images

A yau Laraba ne ake bukin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta Malaria a duniya, ya yin da ya rage shekaru uku a cim ma muradun karni na magance cutar duniya. Amma rahotanni na cewa, akalla yara 300,000 ke mutuwa a shekara sanadiyar zazzabin cizon sauro a Najeriya.

Talla

cutar cizon saur0, na sanadiyar mutuwar mutane Miliyan uku duk shekara a Najeriya, kamar yadda kididdigar Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna. Kuma yawancinsu kananan yara ne.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka kasa samun ci gaba wajen magance matsalar mace-macen kananan yara saboda cutar a shekaru 40 da suka gabata.

Alkalumma sun nuna cewa, kasar ta samu raguwar kashi Goma ne kawai daga cikin yaran da ke mutuwa, sabanin kashi 53 da kasashe irin su Ghana, Kamaru da Kenya suka samu.

Rahoton yace har yanzu akwai aiki babba a wajen hukumomin Gwamnati da jami’an kiwon lafiya da kungiyoyi wajen wayar da kan jama’a don tsabtace muhalli, tare da sanya mata da yara amfani da gidan sauro mai dauke da magani,
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.