Nigeria-Yobe-Hari-Kasuwa

Akalla sama da mutane 34 zuwa 50 ne suka rasa rayukansu a wani hari a kasuwar Patiskum a jahar Yobe

A kalla mutane 34 ne suka rasa rayukansu a cikin wani harin Bam da aka kai a wata kasuwa dake garin Patiskum na jahar Yobe, a yankin arewacin tarayyar Nigeriya, kamar yadda majiyoyin gwamnatin jahar Yobe, da na shaidun gani da ido suka tabbatar, inda aka bayyana cewa, yawan mutane da suka rana rayukansu na iya karuwa.

Talla

Shugaban ma’aikatar aikin ceto ta jahar ya ce, a na zaton mutane da suka hallaka a harin da aka kai a marecen jiya laraba zasu kai 50.

Majiyar ta kara da cewa, yanzu haka dai mutane 22 ne suka jikkata.

harin ya biyo bayan wani samame ne da wasu yan tsagera suka kai a kasuwar, bayan da yan kasuwar suka yi nasarar korar wasu barayi da suka yi niyar rabasu da dukiyoyinsu, tare da kama daya daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.