Najeriya

Har yanzu ana zaman dar-dar a Potiskum

MD Abubakar Sabon Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya
MD Abubakar Sabon Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya RFI Hausa

Rahotanni daga garin Potiskum dake jihar Yobe a Nigeria na cewa hankulan matasan garin ya tashi matuka sakamakon zargin da sukeyi, wa jami'an tsaron hadin guiwa dake garin, na hannu tsundum wajen kisan bayin Allah samada 60 makon jiya.Al'amura sun tsaya cif a garin na Potiskum, sakamakon matasan garin da suka hau manyan titunan jihar, inda suke kone tayu a garin.Matasan suna nuna fushin su ne kan yadda haryanzu aka gagara zakulo wadanda suka yi aika aikar kisan kan jama'a da aka yi a makon da ya wuce.Yanzu haka dai lamura sun tsaya cik a garin don kuwa yanzu haka ba shiga ba fita.