Rashidi Yekini na Najeriya ya mutu yana da shekaru 48

Sauti 07:05
Rashidi Yekini lokacin a cikin ragar Bulgeria bayan zira kwallon shi ta farko a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka a shekarar 1994
Rashidi Yekini lokacin a cikin ragar Bulgeria bayan zira kwallon shi ta farko a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka a shekarar 1994 Nigerian Vanguard

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi bayani ne game da Rashidi Yakini tsohon dan wasan Super Eagle a Najeriya wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Juma’a 4 ga watan Mayu yana da shekaru 48 bayan kwashe lokaci yana jinyar rashin lafiya.

Talla

Rashidi Yekini yana cikin manyan ‘Yan wasan da suka kafa tarihi a Najeriya kuma tarihin Super Eagle ba zai taba kammaluwa ba tare da sunan Rashidi Yekeini ba.

Rashidi Yekini shi ne dan wasan Super Eagle da yafi yawan zira kwallaye a raga, domin ya zira wa Najeriya kwallaye 37 a wasanni 58 daya bugawa kasar shi.

Rashidi Yekini shi ne dan wasan da ya fara zira wa Najeriya kwallo a tarihin gasar cin kofin Duniya da Najeriya ta kai ziyara a kasar Amurka a shekarar 1994, a wasan Farko da Najeriya ta lallasa Bulgeria ci 3-0.

Rashidi Yekni kuma shi ne dan wasa na farko da ya fara karbar kyautar gwarzon dan wasan Afrika a Najeriya.

‘Yan wasa da dama sun yi juyayin mutuwar Rashidi Yekini tare da adduar’ Allah ya jikan shi.

Akwai Abdulfatayi Yekini da ya yi tashe tare da Rashidi Yakini a zamanin da wadanda suka yi wasa tare kuma Abdulfatayi Yekini ya shaida wa shirin Duniyar Wasanni cewa Rashidi Yekini kamar dan uwa ne a wajen shi tare da bayyana cewa Rashidi Yakini mutum ne mai son taimakawa mutane.

Adamu Jeje Tsohon dan wasan Super Eagle yace yana da wahala Najeriya ta sake samun dan wasan mai cin kwallo a raga kamar Rashidi Yekini.

Tuni dai hukumar CAF da ke kula da kwallon kafa a Afrika ta aiko da sakon ta’aziya ga iyalan Yekini, inda shugaban Hukumar Issa Hayatou yace ba zasu taba mantawa da gudummuwar Yekini ga ci gaban kwallon kafa a Afrika.

Jana’izar Rashidi Yekini ta samu halartar abokan wasan shi irinsu Adepujo da Ike Shorumu da Ademola adeshina.

Yanzu haka kuma kungiyar tsoffin ‘yan wasan kwallon kafa a Najeriya karkashin jagorancin Dahiru Sadi ta bukaci hukumar NFF ta karrama sunan Rashidi Yekeni domin saka suna shi a filin wasa ko wani babban wuri da ya shafi kwallon kafa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.