Najeriya

Wani bom ya tashi a Kwalejin ilimi da ke Kano

kofar shiga Jami'ar Bayero  da ke Kano
kofar shiga Jami'ar Bayero da ke Kano REUTERS/Stringer

Rahotanni daga Kano a Nigeria na cewa wani bom ya tashi a Kwalejin Ilimi da ke birnin Kano. A yau din dai saura kadan wasu bama-bamai da aka dasa a Jamiar Bayero ta Kano su tashi, kuma an warware sunkin bama-baman biyu kafin su tashi.Rahotanni na cewa an sami bama-baman ne a sashen nazarin kimiyya dake jamiar.Bayanan na cewa jami’an tsaron jami’ar ne suka fara ganin kunshin kafin su sanar da ‘yan sanda.Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Idris ya gaskata cewa ma’aikatan sa suka kashe karfin bam din, domin kuwa bai tashi ba.