Yajin aikin likitoci a Nigeria da korar likitoci a Lagos

Sauti 18:05
Marasa lafiya na cikin wani hali a Nigeria
Marasa lafiya na cikin wani hali a Nigeria Reuters/St-Felix Evens

GWAMNATIN Jihar Lagos a Nigeria, ta sanar da korar likitoci 788 daga aiki, saboda kin amsa takardun tuhumar da aka musu na zuwa yajin aiki.An dai dauki watanni ana dauki ba dadi tsakanin likitocin da Gwamnati kan Karin albashi, abinda ya tilasta musu zuwa yajin aiki.Yanzu haka al’ummar Jihar Lagos na cikin halin kakanikayi tun lokacin da likitocin suka shiga yajin aikin.wanna shine batun da za mu duba a cikin shirin na yau, wanda Mahmud Lalo zai Gabatar.