Dakta Muhammed Ali Pate

Sauti 03:03
Dakta Muhammed Ali Pate Ministan Lafiya a Najeriya
Dakta Muhammed Ali Pate Ministan Lafiya a Najeriya

Ma’aikatan Lafiya a Najeriya sun tsunduma cikin yajin aikin gama-gari, saboda kin biya musu bukatun su da Gwamnatin kasar ta yi. Wannan kuma na zuwan ne kwana daya da korar Likitoci kusan 800 da gwamnatin Lagos ta yi saboda yajin aikin da suka kwashe makwanni suna gudanarwa saboda neman karin karin albashi. Dakta Muhammed Ali Pate shi ne Ministan Lafiya kuma ya yi bayani daga bangaen gwamnati.