Nigeria
An mayar wa alkalin kotun daukaka karar Nigeria mukamin shi
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar kula da lamuran Shari’ah a Nigeria ta dawo da alkalin kotun daukaka karar kasar, mai shari’ah Ayo Salami kan mukamin shi. A watan Augustan bara aka dakatar da shi, sakamakon kin neman afuwar tsohon babban jojin kasar Aloysius Katsina-Alu, saboda wata sa-in-sa da ta shiga tsakanin su.Mai shari’ah Ayo salami ya zargi tsohon babban jojin da neman ya bi bayan Gwamnan Jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wamako, yayin yanke hukunci kan wata karar da aka kai gaban shi.