Nigeria

Yara na cikin kasadar shakar gubar dalma

wani mahaki darma a jahar Zamfara
wani mahaki darma a jahar Zamfara

KUNGIYAR likitoci ta duniya Doctors Without Borders tace fiye da yara kanana dubu dubu daya da dari 5, sun shaki gubar dalma a kauyen Bajega da ke jihar zamfara a taraiyyar Nigeria. Shugaban kungiyar, wadda da ke da cibiyar ta birnin Geneva, Ivan Gaytonya da ke Magana da manema labaru a birnin Abuja ya ce akwai yara fiye da dubu 4 da ke kasadar shakar gubar.Sai dai Gaytonya yace ana kokarin yashe kasar garin, da ke sanya yaran cikin hadari.