Najeriya

Shinkafi ya karyata zargin canza sheka zuwa ANPP a Zamfara

Tsohon Gwamnan Jahar Zamfara Alh. Mahmuda aliyu Shinkafi
Tsohon Gwamnan Jahar Zamfara Alh. Mahmuda aliyu Shinkafi This Day

Tsohon Gwamnan Jahar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi ya karyata jita jitar da ake yi akan ya canza sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa Jama’iyyar ANPP mai mulki a Jahar. Bayan wani rahoto da aka nuna hoton tsohon gwamnan tare da bayani akan yunkurin canza sheka zuwa tsohowar Jam’iyyarsa.

Talla

Tsohon Gwamnan Jahar Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi

A cewar Mahmuda Shinkafi babu gaskiya ga labarin, illa an rubuta labarin ne domin bata ma shi suna. Amma yace yana nan cikin Jam’iyyar PDP da shi da mutanen shi.

Bayan kwashe wa’adi biyu a matsayin mataimakin Gwamnan Jahar Zamfara, a zaben 2007 ne aka zabi Mahmuda shinkafi matsayin Gwamnan Jahar karkashin Tutar Jam’iyyar ANPP. Daga bisani ne ya canza sheka zuwa Jam’iyyar PDP saboda samun sabani tsakanin shi da Ahmed Sani Yariman Bakura.

Sai dai Mahmuda ya sha kaye a zaben 2011, inda Zamfarawa suka juya ma shi baya suka zabi Alhaji Abdul’aziz Yari Mafara karkashin Jam’iyyar ANPP.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.