Dan Masanin Kano, Dakta Yusuf Maitama Sule

Sauti 04:31
Dan Masanin Kano, Dr. Yusuf Maitama Sule a Lokacin da yake Hira da Rediyon Faransa
Dan Masanin Kano, Dr. Yusuf Maitama Sule a Lokacin da yake Hira da Rediyon Faransa RFIHausa/bashir

A makon gobe ne Najeriya za ta yi bukin cika shekaru 13 da dawowa mulkin Demokradiya, Kuma yanzu haka ana ci gaba da nazarin ci gaban da aka samu, da kuma matsalolin da ake fuskanta. A lokacin da ya ke gabatar da wata kasida game da tsarin Gwamnatin da ya dace da kasashen Afrika, Tsohon Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Dakta Yusuf Maitama Sule, Dan Masanin Kano, ya bukaci gwamnati mai ci sauka daga karagar mulki watanni shida kafin zabe, don bai wa wadanda ba ‘Yan siyasa ba, damar gudanar da zabe, domin kaucewa magudi.

Talla

Barista Solomon Dalung yace Dan Masani ya ba da misalin makiyayi a matsayin shugaba na gari wanda zai hanawa cikin shi ya ba dabbobin da ya ke kiyo.

A cewar Dan Masani sai shugaba ya zama kamar Bafulatani da Dabbobinsa. kuma a cewar shi, kama-karya da Jan Ido da Barazana ba zasu kawo zaman lafiya ba kuma ba za su warware rikici ba sai idan shugaba ya yi kokarin mallakar zukatan mutane kamar yadda Bafulatani ke yin adalci ga dabbobin shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.