Kwallon Kafa

Super Eagle na Najeriya sun sha kashi a Peru

'Yan wasan Super Eagle na Najeriya
'Yan wasan Super Eagle na Najeriya Reuters

‘Yan wasan Super Eagle na Najeriya sun sha kashi ci 1-0 da safiyar Alhamis a kasar Peru. A filin wasa na Estadio National ne kasar Peru ta samu galabar ‘Yan wasan Stephen Keshi na Najeriya.Keshi ya yi amfani ne da matasa masu taka kwallo a gida ba tare da yin amfani da ‘yan wasan da ke taka kwallo a kasashen waje ba.