Tanzaniya

A kasar Tanzaniya an jefe mutane 3000 har lahira bisa zargin su da maita

RFI

A kasar Tanzaniya akalla mutane 3.000 da ake zargi da maita, mafi yawancinsu masu girman shekaru aka jefe har lahira a cikin shekaru 6 da suka gabata, kamar yadda wani rahoto na kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar ya nunar.

Talla

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Legal and Human Rights Center, LHRC), a cikin rahoton da ta aikawa kamfanin dillancin labaran AFP a yau talata, ta bayyana cewa, tsakanin shekara ta 2005 zuwa 2011 mutane dubu 3.000 makwabtansu suka jefe har lahira, bayan da suka zargesu da ayukan maita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.