Alhaji Faruk Adamu Aliyu, ya kare Buhari

Sauti 04:24
Janar Muhammadu Buhari Tsohon shugaban Najeriya
Janar Muhammadu Buhari Tsohon shugaban Najeriya rfihausa

Alhaji Faruk Adamu Aliyu, Dan takaran Gwamnan Jahar jigawa karkashin Tutar Jam’iyyar CPC ya mayar da martani ga kalaman Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido wanda yace Janar Muhammadu Buhari sabon Dan siyasa ne, tare da ba Buhari shawarar tauna furucinsa kafin yin wata Magana. A Hirar shi da Rediyo Faransa, Hon. Faruk ya bukaci Sule Lamido bayyana kadarorin da ya mallaka.