Najeriya-Jamus

Wani dan kasar Jamus ya rasa ransa a cikin masayar wutar neman kwato shi daga wadanda suka yi garkuwa dashi a Najeriya

© RFI

RAHOTANNI dagabirnin Kano, dake Nigeria, sun ce wani Dan kasar Jamus, Edgar Raupach, da akayi garkuwa da shi, ya rasa ransa, yayin da jami’an tsaro suka kaddamar yunkurin ceto shi yau da asuba.

Talla

Bayanan dake zuwa daga Kanon, sun ce, bayan Ba Jamushen, wasu mutane biyar sun rasa rayukansu, yayin da kuma aka kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da sace shi.

Mazauna unguwar da akayi garkuwa da shi a Kanon, sun ce sun ji karar fashe fashe da kuma manyan makamai, lokacin da jami’an tsaro suka yiwa gidan kawanya.

A wani labari kuma, gwamnatin kasar Italy, ta sanar da sace wani injiniya Dan kasar a Jihar Kwara, dake Nigerian.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.