Lafiya

Bincike ya nuna za’a samu yaduwar Cutar Sankara da kashi 75 a 2030

Wata Majinyaciyar Cutar Sankara a kasar China.
Wata Majinyaciyar Cutar Sankara a kasar China. REUTERS/Stringer

Wata Mujallar bincike mai suna Lancet Oncology, ta fitar da wani rahoto wanda ya bayyana hasashen nan da shekarar 2030, za’a samu karuwar cutar Sankara da kashi 75 a Duniya.

Talla

Wani gungun masana daga hukumar kasa-da-kasa mai binciken cutuka masu nasaba da cutar Daji, ta Sankara a karkashin jagorancin Freddie Bray, suka ce a shekarar 2008 an samu wasu sabbin mutane masu fama da cutar Sankara Miliyan 12.7, inda kuma aka bayyaba zasu karu zuwa Miliyan 22.2 nan da 2030.

Binciken masanan ya nuna kashi 90 na masu cutar na karuwa ne daga matalautan kasashe.

Mafi yawancin cutar da ake samu daga kasashe daban-daban sun hada da cutar Sankarar Mama, da Sankarar Mahaifa wadanda dukkaninsu suna da nasaba da abinci irin na turawa.

A kasashe masu tasowa nau’in Cutar sankara da aka samu a 2008 sun hada da Sankarar Mama da Huhu.

Amma a kasashe masu raunin tattalin arzikian fi samun Sankarar Makoshi, da Ciki, da Huhu da kuma Hanta.

A daukacin kasashen dai an lura da samun raguwar Cutar sankara da wasu halittun Mahaifa da Ciki, a shekarun da suka gabata.

Amma a kasashe matalauta cutar Sankarar mahaifa ta fi ta’azzara idan aka kwatanta da Sankarar Mama da Hanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI