CAN 2013

Najeriya da Kamaru suna da fatar shiga gasar Afrika a badi

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya
'Yan wasan Super Eagles na Najeriya Reuters

Kamaru da Najeriya sun fara huce hushin bara bayan samun nasarar wasannin neman shiga gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a karshen mako inda Kasar Kamaru ta samu nasarar doke kasar Guinea Bissau ci 1-0 a birnin Yawunde, Najeriya kuma ta doke Rwanda ci 2-0.

Talla

A gasar cin kofin Afrika da aka gudanr a shekarar a bana, kasashen Biyu basu samu shiga gasar ba. Amma Yanzu haka ‘Yan wasan Super Eagle na Najeriya da Indomitable Lions na Kamaru sun tsallake zagaye na gaba.

Sauran kasashen da kuma suka tsallake zuwa fafatawa ta gaba sun hada da Malawi da Saliyo da Uganda da Liberia inda zasu gamu da kasashen da suka buga gasar cin kofin Afrika a Gabon da Equatorial Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.