Shirin lafiya jari a wannan mako ya tattauna ne akan muhimmancin shayar da nonon uwa tsantsa ga jarirai na tsawon watanni shida, wanda likitoci suka bayyana cewa ya na kare Yara daga kamuwa daga cututtuka da dama. Shirin ya tattauna da likitoci ne daga Jamhuriyar Nijar, da wasu manyan jami’an gwamnati akan batun.
Sauran kashi-kashi
-
Lafiya Jari ce Ya kamata a rika daukar cutar makero da muhimmanci - Kwararru Shirin na wannan mako zai maida hankali ne kan cutar makero, guda cikin cutukan fatar da ke matsayin ruwan dare a wannan lokaci musamman tsakanin kananan yara.29/05/2023 09:59
-
Lafiya Jari ce Yadda karancin takardun Naira ya shafi mara lafiya a asibitocin Najeriya Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba yadda matsalar sauya wasu takardun kudin Nairar Najeriya da tsadar rayuwa suka shafi harkokin asibiti masamman majinyata ko masu bukatar gaggawa a asibiti.10/04/2023 10:08
-
Lafiya Jari ce Ta'ammuli da miyagun kwayoyi na kara yawan masu tabin hankali a Nijar Shirin "Lafiya jari ce" na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsalar shaye-shaye sannu a hankali ke ci gaba da jefa tarin matasa a lalurar hauka ko kuma tabin hankali, matsalar da ke ci gaba da tsananta a sassan Jamhuriyya Nijar musamman tsakanin matasa ko kuma daliban jami’o’i. Alkaluman ma’aikatar lafiyar Nijar na nuna yadda ake da tarin matasa da yanzu haka ke karbar maganin cutar kwakwalwa galibinsu sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi ko kuma shaye-shayen zamani.13/03/2023 10:18
-
Lafiya Jari ce Yadda jama'a za su bai wa lafiyarsu kariya a lokacin zabe Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wanna mako ya kawo mana yadda jama'a za su duba lafiyarsu ne a lakcin zabuka. Wannnan maudu'i na zuwa ne bisa la'akari da yadda jama'a da dama suka samu rauni, wasu kuma suka mutu saboda tarzomar da ta tashi a lokacin zaben shugaban kasa a Najeriya.06/03/2023 10:07
-
Lafiya Jari ce An samu karuwar cutar Gout a tsakanin 'yan Najeriya Shirin Lafiya Jari Ce na wannan lokaci ya tattauna akan cutar Gout da ke kumbura sassan jikin Dan Adam ciki kuwa har da jjijiyoyi.20/02/2023 10:22