Gwamnoni Shida da ke yankin Arewa maso Gabas, sun cim ma wata yarjejeniya neman lasisin samun albarkatun man Fetur daga gwamnatin tarayya, domin fara aikin hako Man a yankin da masana ke cewa yana da arzikin ma'adanai a karkashin kasa. Gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya yi wa wakilin RFI Shehu Saulawa karin bayanin inda aka kwana kan wannan batu.