Shirin Lafiya Jari ya yi bayani akan muhimmancin gwajin jini ga ma'aurata kafin aure, inda muka tattauna da masana da kuma wasu magidanta.
Sauran kashi-kashi
-
Lafiya Jari ce Yadda karancin takardun Naira ya shafi mara lafiya a asibitocin Najeriya Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba yadda matsalar sauya wasu takardun kudin Nairar Najeriya da tsadar rayuwa suka shafi harkokin asibiti masamman majinyata ko masu bukatar gaggawa a asibiti.10/04/2023 10:08
-
Lafiya Jari ce Ta'ammuli da miyagun kwayoyi na kara yawan masu tabin hankali a Nijar Shirin "Lafiya jari ce" na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsalar shaye-shaye sannu a hankali ke ci gaba da jefa tarin matasa a lalurar hauka ko kuma tabin hankali, matsalar da ke ci gaba da tsananta a sassan Jamhuriyya Nijar musamman tsakanin matasa ko kuma daliban jami’o’i. Alkaluman ma’aikatar lafiyar Nijar na nuna yadda ake da tarin matasa da yanzu haka ke karbar maganin cutar kwakwalwa galibinsu sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi ko kuma shaye-shayen zamani.13/03/2023 10:18
-
Lafiya Jari ce Yadda jama'a za su bai wa lafiyarsu kariya a lokacin zabe Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wanna mako ya kawo mana yadda jama'a za su duba lafiyarsu ne a lakcin zabuka. Wannnan maudu'i na zuwa ne bisa la'akari da yadda jama'a da dama suka samu rauni, wasu kuma suka mutu saboda tarzomar da ta tashi a lokacin zaben shugaban kasa a Najeriya.06/03/2023 10:07
-
Lafiya Jari ce An samu karuwar cutar Gout a tsakanin 'yan Najeriya Shirin Lafiya Jari Ce na wannan lokaci ya tattauna akan cutar Gout da ke kumbura sassan jikin Dan Adam ciki kuwa har da jjijiyoyi.20/02/2023 10:22
-
Lafiya Jari ce Asibitocin Najeriya za su fara amfani da tsarin neman ganin likita ta wayar Salula Shirin lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba wani ci gaban lafiya da aka samu a Najeriya bayan da hadaka tsakanin ma'aikatar lafiya da hukumar sadarwa ya kai ga samar da wata manhaja wadda za ta saukakawa marasa lafiya samun damar ganin likita tun gabanin su je asibiti, a wani yunkuri na dakile cunkoson da ake samu a asibitocin kasar.06/02/2023 10:00