Najeriya

An sake gurfanar da Henry Okah a kotun Afrika ta Kudu

Henry Okah, a lokacin d aka gurfanar da shi a kotu Afrika ta Kudu a shekarar 2010
Henry Okah, a lokacin d aka gurfanar da shi a kotu Afrika ta Kudu a shekarar 2010 AFP PHOTO / PABALLO THEKISO

An sake gurfanar da Henry Okah, mutumin da ake zargi da shirya kai hari lokacin bikin cika shekaru 50 da ‘yancin kan Nigeria a Abuja, a kasar Afrika ta kudu. Ministan Nigeria dake kula da Yankin Niger Delta, Godsday Orubebe na daga cikin shaidun farko da suka yi bayani a gaban kotun, inda ya tabbatar da hannun Okah a harin da aka kai. 

Talla

An dauki kwararan matakan tsaro wajen shari’ar.

Wanda ya fara bada bahasi a gaba kotun, Orubebe ne, inda ya zargin cewa Okah kusa ne a kungiyar mai fafatukar neman ‘yancin yankin Niger Delta, ta MEND wacce ta dauki alhakin kai harin na Oktoban shekarar 2010.
 

Kasar Afrika ta Kudu dai na sauraran karar a domin tabbatar da dokar nan ta kasada kasa, saboda kuma Najeriya bat a nemi a mika Okah zuwa kasarta ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI