Nijeriya

Sojoji sun yi ikirarin kashe 'yan bindiga 30 a Jihar Yobe

Soja na sa ido kan tsaro a arewacin Nigeria
Soja na sa ido kan tsaro a arewacin Nigeria REUTERS/Afolabi Sotunde

Rundunar  da ke aikin samar da tsaro a Jihar Yobe, ta sanar da kashe Yan bindiga 30 da ake zargin 'Yan kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad ne, da ake kira Boko Haram, cikin su har da shugaban su guda.Mai Magana da yawun rundunar Lt Lazaruns Eli ya tabbatar da lamarion, sai dai har yanzu kungiyar ta Boko Haram ba ta ce uffan kan batun ba.