Najeriya

Jami'an tsaro sun killace wasu yankunan birnin Lagos

Sojoji a kan hanya a Nigeria
Sojoji a kan hanya a Nigeria sphotos-a.xx.fbcdn.net

A birnin Lagos din Tarayyar Nigeria, dubun dubatar mutane na can suna ta tattaki zuwa wuraran aikin su, sakamakon rashin ababen hawa, bayan da jami’an tsaron kasar suka killace wasu manya titinunan birnin. Har yanzu dai ba bayanai, kan dalilan rurrufe hanyoyin da suka shiga anguwannin Ikoyi da Victoriya Island.Yanzu haka mazauna birnin na can suna neman wasu hanyoyin zuwa wuraren harkokin su, yayin da kiristoci ke shirye-shiryen bukukuwan kirsimeti a gobe Talata.Wakilin mu, ya ji mutane da dama suna guna-guni kan wannan matakin da jami’an tsaron suka dauka, yayin da aka ga wasu jami’an tsaron na zare wa masu tafiya da kafa idanu.