Faransa-Afrika

'Yan uwan bafaranshen da aka sace arewacin Najeriya sun nemi a gaggauta sakin sa

‘Yan uwan bafaranshen nan da aka sace a cikin jihar Katsina da ke arewacin tarayyar Najeriya ranar 19 ga wannan wata na Disamba mai suna Collomp Francis, sun yi kira ga wadanda ke garkuwa da shi da su sake shi saboda a cewarsu yana fama da wani rashin lafiyar da ke bukatar a rika kula da lafiyarsa a kai-a-kai.

Talla

A wani faifan bidiyo da aka watsa a yau litinin, Gilba Marbois wadda Francis ke aure da ‘yar uwarta, ta ce ina ‘’mai kira ga wadanda ke garkuwa da collomp Francis da su sake shi, saboda a halin yanzu kanwata na a cikin bakin cikin juyayin halin da mijinta ke ciki.

Matar dai ta tunatar da cewa Francis wanda kwararren injniya ne da ke aiki da wani kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da hasken rana, dan kimanin shekaru 63 ne a duniya, yana fama da ciwon zuciyar da ke bukatar kulawar likitoci a ko da yaushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.