WHO
Hukumar lafiya ta duniya tace an samu raguwar matuwar yara
Wallafawa ranar:
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta bayyana cewa, an samu raguwar mace-macen yara kanana, da ciwon Bakon Dauro ke kashewa a duniya, da fiye da kashi 70 cikin dari a shekaru goma da suka gabata. Hukumar, tace hakan yana da nasaba da irin cigaban da aka samu ta fannin karuwar magungunan cutar.