Najeriya

Keshi ya janye marabus din shi, zai ci gaba aikin horar da Super Eagles

Kocin Super Eagles na Najeriya Stephen Keshi.
Kocin Super Eagles na Najeriya Stephen Keshi. REUTERS/Thomas Mukoya

Kocin Super Eagles Stephen Keshi ya janye Marabus daga aikin horar da ‘Yan Wasan Super Eagles bayan taimakawa Najeriya lashe kofin Afrika karo na uku.A wata yarjejeniya da Kocin ya sanya wa hannu daga Hukumar kwallon Najeriya ta NFF, Keshi yace zai ci gaba da aikin horar da Super Eagles bayan Ministan wasanni kasar ya shiga tsakanin rikicin da ke tsakanin shi da shugabannin hukumar.

Talla

“Ina mai bayyana bacin rai akan wasu batutuwa da suka taso a lokacin gasar cin kofin Afrika da muka lashe da ikon Allah. Don haka na janye murabus di na, zan ci gaba da aikin horar da Super Eagles.” Inji Keshi.

Bayan saka hannu ga yarjejeniyar, Stephen Keshi ya godewa Ministan Wasanni Malam Bolaji Abdullahi saboda shiga tsakanin sasantawa da NFF.

A watan Nuwamba shekarar 2011 ne Keshi ya karbi aikin horar da Super Eagles bayan Sallamar Samson Siasia.

Akwai buki na musamman da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya hada domin tarbar ‘Yan wasan Super Eagles a fadar shi da ke Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.