Nigeria

Gwamnan Jihar Bauchi ya fice daga Kungiyar Gwamnoni

Malam Isa Yuguda Gwamnan Jahar Bauchi
Malam Isa Yuguda Gwamnan Jahar Bauchi RFI Hausa/Tanko

BISA Dukkan alamu rikicin da ta kutsa kai kungiyar Gwamnonin Nigeria bata kare ba, inda Gwamnan Jiahr Bauchi, Malam Isa Yuguda ya sanar da ficewar sa daga kungiyar saboda abinda ya kira munafunci.Gwamnan wanda yake tattaunawa da wakilinmun dake Bauchi Shehu Saulawa yace babu abinda zai sa ya sake halartan taron Gwamnoni muddin ba’a sasanta wannan takaddamar ba.Yace dukkan Gwamnonin arewa suka amince da zaben Gwamnan jihar Filato Jonah Jang ya jagorancesu, saboda haka babu wani dalili da zai sa wasu su zame daga baya.