Najeriya

PDP ta dakatar da Wammako

Gwamman Jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wamakko
Gwamman Jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wamakko thenation

Jama’iyyar PDP a Nigeria, ta sanar da dakatar da Gwamnan Jihar Sokoto, Dr Aliyu Magatakarda Wammako, saboda abinda ta kira, kin amsa gayyatar da ake masa da kuma watsi da umurnin Jam’iyar.Sakataren yada labaran jam’iyar, Chief Olisa Metuh ya sanar da matsayin, bayan taron shugabanin Jam’iyar.Kokarin jin ta bakin mataimakin shugaban Jam’iyar na kasa, Amb Ibrahim Kazaure da kuma jami’an Gwamnatin Sokoto ya ci tura.Wammako ne na biyu a jerin gwamnonin da jama’iyyar ta PDP ta kora a baya bayan nan, don makonni 2 da suka gabata jama’iyyar ta sallami shugaban kungiyar Gwamnonin kasar kuma gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amechi.