Wasan Tennis

Rolland Garros: Buga wasan karshe tsakanin Djokovic da Nadal, William da Sharapova

Novak Djokovic (Hagu) da Serena Williams (Dama)
Novak Djokovic (Hagu) da Serena Williams (Dama)

A yau Novak Djokovic da Rafael Nadal za su kara a wasan karshe na a fagen gasar Rolland Garros ko kuma French Open. Djokovic wanda shine na daya a duniya, na bukatar lashe wannan kofi ne domin ya zamanto dan wasan Tennis na 8 da ya lashe dukkanin manyan gasa a fagen wasan Tennis a duniya.  

Talla

Nadal a daya bangaren, idan har ya lashe zai kasance dan wasan Tennis na farko a duniya da ya lashe wannan kofi a karo na takwas.

A bangaren mata kuwa Maria Sharapova ta samu damar shiga zagaye na karshe a fagen gasar.

Wannan nasara ta samu ne bayan ta doke Victoria Azarenka 'yar kasar Belarus da ci 6-1, 2-6 da kuma 6-4.

Za ta kuma buga wasanta na karshe a ranar Asabar da Serena Williams ‘yar kasar Amurka wacce ta doke Sara Errani ‘yar kasar Italiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.