Cote d'Ivoire

Cote d’ Ivoir na ci gaba da rike matsayi na farko a iya taka kwallo a Afrika

Dan wasan Cote d'Ivoir, Didier Drogba
Dan wasan Cote d'Ivoir, Didier Drogba REUTERS/Mike Hutchings

Hukumar kwallon kafa ta duniya, wato FIFA ta fitar da jerin sunayen kasashen da suka fi iya taka kwallo a Nahiyar Afrika.

Talla

Inda kasar Cote d’Ivoir ke ci gaba da rike matsayi na farko a Afrika take kuma rike da matsayi na 13 a duniya.

Kasar Ghana ce dai ta biyu a Afrika kana itace ta 21 a duniya a yayin da Mali ke jeri na uku a Afrika take kuma jeri na 23 a duniya.

Najeriya dai ita ce ta hudu a Afrika ita ce kuma ta 31 a duniya.

Kamaru dai na jeri na 12 a Afrika tana kuma jeri na 65 a duniya a yayin da Nijar kuma ke jeri na 30 a Afrika kana tana jeri na 107 a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI