Syria

Rasha ta bayyana damuwarta game da kwararar mayakan sa –kai zuwa Syria

Kasar Rasha ta bayyana damuwarta dangane da yadda mayakan sa-kai ke ci gaba da kwarara zuwa Siriya domin taimakawa ‘yan tawaye da ke fada sojojin Bashar Assad.

Talla

Shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Tarayyar Rasha Alexandre Bort-nikov, ya ce sun damu matuka sakamakon yadda aka samu ‘yan asalin yankin Caucause da ke neman ballewa daga kasar su akalla 200 a cikin jerin mayaka ‘yan asalin kasashen ketare da ke marawa Alqa’ida baya a yakin da take yi dakarun Bashar Assad.

Babban abin damuwa ga kasar ta Rasha a wannan batu dai, shi ne yadda tsoffin ‘yan tawaye da ta kira su da suna ‘yan ta’adda daga yankin Chencheniya a fagen dagar kasar ta Syria, inda Alexendre din ya ce fargabarsu ita ce irin salon gwagwarmayar da wadannan mutane za su dawo da shi a Rasha bayan kammala yakin na Syria.

Tun da jimawa ne dai aka tabbatar da cewa akwai mayaka ‘yan asalin kasashen ketare cikinsu kuwa har da ‘yan Alqa’ida da ke marawa ‘yan tawayen Syria baya a wannan fada, yayin da shi kuma Bashar al- Assad ke samun taimakon ‘yan tawaye cikinsu kuwa har da mayakan kungiyar nan ta Hizbullah da ke kasar Labanan.

To sai dai duk da irin mummunan sakamakon da manazarta ke hasashen hakan zai iya haifar wa sauran kasashe ta fannin tsaro bayan kammala wannan yaki na Syria, duniya ta zura ido ba tare da yin wani abu dangane da hakan ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI