Rasha

Shugaban Rasha ya bayyana rabuwa da matarsa

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin tare da matarsa
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin tare da matarsa REUTERS/Michael Klimentyev/RIA Novosti/Kremlin

Shugaban Kasar Russia, Vladimir Putin, ya sanar da rabuwa da matar sa, Lyudmilla, da suka kwashe shekaru 30 suna tare, saboda abinda ya kira rashin jituwa a tsakanin su.

Talla

Putin ya shaidawa manema labarai cewar, tare da matar suka cimma matsayar rabuwar, ganin cewar ba sa iya zama inuwa guda.

Rahotanni na nuna cewa an jima ana jin rade radin cewa ma’auratan na shirin rabuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI