Jamus

Ambaliyar Ruwa: Jamus da Hungary na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana

An kwashe mutane a wani yanki da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Argentina
An kwashe mutane a wani yanki da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Argentina

Kasashen Jamus da kuma Hungry na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana, a daidai lokacin da masu hasashen yanayi ke cewa akwai yiyuwar ambaliyar ruwan da ta shafi wasu kasashe na gabashin Nahiyar Turai kan iya afkwa wadannan kasashe a nan gaba kadan.

Talla

Tuni dai ruwan sama mai karfin gaske da aka shatata a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 10 a kasashen na gabashin Turai mafi yawansu a Jamhuriyar Czech.

Wasu daga cikin matakan da hukumomi ke dauka a kasar ta Jamus da kuma Hongry sun hada har da kwashe jama’a daga yankunan da ake zaton cewa ambaliyar za ta iya shafa zuwa wasu wurare na daban, yayin da a aka sanya jami’an tsaro da kuma ma’aikatan agaji ke kasancewa cikin shiri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.