Syria

MDD ta bukaci hukumomin Syria su ba da damar shiga yankin Qusayr

Wani magoyin bayan shugaba Bashar al Assad dauke da tutar kasar
Wani magoyin bayan shugaba Bashar al Assad dauke da tutar kasar REUTERS/Mohammed Azakir

Kwanitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci gwamnatin kasar Syria da ta bai wa kungiyoyin agaji na kasa da kasa damar shiga yankin Qusayr, wanda dakarun gwamnatin suka kwace daga hannun ‘yan tawaye domin kai wa jama’ar yankin taimakon gaggawa.

Talla

Kiran ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar ke cewa za ta kafa wata gidauniya don tara kudaden da yawansu zai kai dalar Amurka miliyan dubu 5,200, domin taimakawa mutane akalla miliyan 10 da ke fama da matsaloli sakamakon yakin da ake yi a kasar ta Syria.

Bayan share tsawon makwanni uku ana fafatawa, dakarun gwamnatin Bashar al Assad da ke samun goyon bayan mayakan kungiyar Hizbullah daga kasar Lebanon, sun samu nasarar fatattakar ‘yan tawaye da ke samun goyon bayan manyan kasashen duniya daga birnin na Qusayr mai matukar muhimmanci ga ‘yan tawayen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI