Saudiya

Mutane 31 sun mutu a Saudi Arabiya sanadiyar kamuwa da cutar mashako

Sarki Abdallah na Saudiya
Sarki Abdallah na Saudiya AFP/Getty Images)

Hukumar Lafiya ta duniya WHO, ta ce kawo yanzu akalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wata sabuwar cutar mashako mai alaka da numfashi wacce ke da tsanani bayan da aka samu karin mutuwar mutum daya a jiya Juma’a a kasar saudia Arabiya.

Talla

Mutum na baya baya nan da ya rasu, ya kamu da cutar ne a ranar 31 ga watan jiya, kuma a jimilce mutane 55 ne suka kamu da cutar yayin da 31 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya.

Rahoton da hukumar ta lafiya ta fitar na cewa, cutar ta fi tsakanta ne a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, da suka hada da Qatar, Saudia Arabiya, Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Tunisia, yayin da aka samu wadanda ke dauke da kwayoyin cutar a kasashen Jamus, Birtaniya, Faransa da kuma Italiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI