Wasan Tennis

Nadal ya doshi lashe kofin Rolland Garros a karo na takwas bayan doke Djokovic

Rafael Nadal.
Rafael Nadal. RFI / Pierre René-Worms

Rafael Nadal ya dauki hanyar lashe kofin gasar Rolland Garros sau takwas bayan ya doke dan wasan Tennis na farko a duniya, Novak Djokovic a wasan daf da na karshe. 

Talla

Djokovic ya sha kayi ne a hanun Nadal da ci 6-4, 3-6, 6-1, 6-7 (3/7).

Nadal wanda shine ke rike da kofin zai kara da David Ferrer zai kasance dan wasan Tennis na farko da zai lashe kofin idan ya samu nasara yayin da Ferrer kuma ya kai wasan karshe a karon farko a babban wasan Tennis na duniya da ake yiwa lakabi da Grand Slam.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.