Afrika ta Kudu

An sake garzayawa da Mandela zuwa asibiti

Motar ba da taimakon gaggawa dauke da Nelson Mandela a hanyarta na zuwa asibiti
Motar ba da taimakon gaggawa dauke da Nelson Mandela a hanyarta na zuwa asibiti

A karo na hudu cikin watannin bakwai, an sake komawa da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela zuwa asibiti cikin wani mawuyacin hali saboda fama da yake yi da ciwon huhu.

Talla

An kwantar da Mandela wanda zai cika shekaru 95 a watan gobe, a asibitin dake Pretoria da sanyin safiyar yau Asabar.

“A ‘yan kwanakin nan ne ciwon tsohon shugaban kasar ya kuma tashi.” Inji Shugaban kasar mai ci a yanzu, Jacob Zuma a wata rubutacciyar sanarwa.

A cewar sanarwar, da misalin karfe 1:30 na safe ne ciwon ya tashi ya yi kuma tsanani inda aka garzaya da shi zuwa asibitin na Pretoria.

A watan Aprilu ne aka sallami Mandela daga asibiti bayan ya kwashe kwanaki goma yana jinya.

A watan Disambar bara ma ya yi jinyar kwanaki 18, wanda shine mafi tsawon lokaci da ya kwashe a asibiti tun bayan sako shi da aka yi daga gidan fursuna a shekarar 1990 kana a aka sake kwantar da shi na kwana daya a watan Maris.

Sanarwar fadar shugaban kasar ta kara bayyana cewa Mandela na samun cikakken kula kamar yadda ya kamata inda “kwararrun likitoci ke kokarin su ga cewa ya samu koshin lafiya.”

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI