Turkiya

Erdogan ya ce bashi da niyyar gudanar da sabon zabe sai a shekarar 2015

Firaministna Turkiya, Recep Tayyip Erdogan
Firaministna Turkiya, Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Osman Orsal

Firaministan kasar, Tayyep Erdogon ya ce ba ya da niyyar kiran zaben gaggawa a kasar ba, kamar dai yadda wasu ‘yan siyasa suka soma nuna bukatar yin hakan da nufin gwada farin jinin da gwamnatinsa ke da shi a cikin al’umma.

Talla

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin Turkiya wacce aka kwashe fiye da mako ana yi a sassa daban daban na kasar.

Wani babban jami’i a jam’iyyar AK ta Erdogon mai suna Huseyin Celik, ya ce za a gudanar da zaben shugaban kasa da kuma sauran zabukan kasar ne a shekara ta 2015 kamar yadda aka tsara.

Jami’in dai yana magana da manema labarai ne jim kadan bayan kammala wani taro da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya gudanar a birnin Ankara, yana mai cewa babban abin da kasar ke bukata a halin yanzu shi ne ci gaba da yin aiki tukuru domin habaka tattalin arzikinta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI