China-Amurka

Obama da Xi sun amince da yin aiki kafada da kafada

Shugaban China, Xi Jingping (Hagu) da takwaransa Barack Obama na Amurka (Dama)
Shugaban China, Xi Jingping (Hagu) da takwaransa Barack Obama na Amurka (Dama) REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka, Barack Obama ya kammala tattaunawa da takwaran aikinsa na kasar China, Xi Jinping inda shugabannin biyu suka amince da yin aiki kafada da kafada domin rage yawan tururin da masana’antunsu ke fitarwa wanda ke taka gagarumar rawa wajen haddasa matsalar gurbatar yanayi a duniya.

Talla

Shugaban China wanda ya share tsawon kwanaki biyu a kasar ta Amurka, ya yi amfani da wannan dama dominn tattaunawa da shugaba Obama kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasashen biyu, cikinsu kuwa har da zargin da suke yi wa junansu na kutsawa a cikin shafukansu na yanar gizo da kuma yadda hakan ke a matsayin barazana ga sha’anin tsaron junansu.

Har ila yau shugabannin biyu sun amince da yin aiki a tare domin gaggauta kwancewa kasar Korea ta Arewa damara, yayin da shugaban kasar China, Xi ya bukaci Amurka da ta dakatar da sayar wa Taiwan da makamai, saboda har yanzu China na kallon kasar a matsayin wani bangare na kasarta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI