Amurka

Wata kungiya za ta raba makamai ga Amurkawa domin su kare kansu

Bindigogin zamani
Bindigogin zamani

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Amurka ta kaddamar da wani shiri da zai tanadi rabawa jama’a makamai domin kare kansu daga masu aikata miyagun laifuka a wasu ungunwanni na birnin Hoston da ke Jihar Texas a kasar.

Talla

Kungiyar mai suna Armed Citizen Project, ta ce a matsayin matakin farko na wannan shiri, mata wadanda ke zaune a unguwanni masu hatsaniya a birnin za ta raba wa bindigogi na zamani domin kare kansu daga mahara.

A cewar kungiyar itace za ta biya kudaden samar da horo ga mutanen dangane da yadda za su sarrafa makaman.

A matakin farko dai mutane akalla 50 ne za su amfana da wannan shiri, yayin da kowace bindiga daya da kuma horon da za a bai wa mutanen, zai tashi akalla dalar Amurka 300.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI